Rahama Sadau ta nemi gafara cikin hawaye

Rahama Sadau

Tauraruwar fina-finan Hausa Rahama Sadau ta nemi gafarar masoya, da ‘yan uwa da abokan arzikinta, dangane da martanin da wani mai bibiyarta ya yi a kan wasu hotuna da ta wallafa a shafukanta na sada zumunta.

Jarumar ta bayyana cikin wani bidiyo da ta wallafa a shafinta na Instagram sanye da Hijabi, cikin kuka da murya mai rawa, tana neman a yafe mata.

”Duk wanda ya sanni, kuma yake bi na, ya san cewa ba zan taba yin wannan abu har cikin zuciya ta ba, hasali ma ban san abun da ya faru ba sai da aka kira ni” a cewarta.

Jarumar ta ce a matsayinta na musulma, ba za ta taba yin wani abu da ta san zai janyo batanci da Anabi Muhammad ba, da alama tana magana ne kan wani da ba musulmi ba da ya alakanta shigar da ta yi a hotunan da addinin musulunci, abin da yasa masu bibiyarta ke zargin ita ce ta janyo faruwar hakan.

”Ko ma menene dai ƙaddara ta riga fata” in ji Sadau, ”amma dai ina mai bawa daukacin al’umma hakuri, don Allah a yi hakuri” ta ci gaba da kuka.

Taurari a ciki da masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood da dama sun fito sun yi Allah-wadai da abin da ya faru.

Ko da a shekarar 2016 ma wani bidiyo da ta taka rawa a cikinsa tare da mawakin gambarar nan Classic ya janyo ce-ce-kuce a shafukan sada zumunta, inda wasu ke cewa abin da ta yi a bidiyon ya saɓa da tarbiyyar a’ummar Arewacin Najeriya.